ALLON SANARWA
Katanga ta kashe 'yan biki 22 a India
Katanga ta kashe 'yan biki 22 a India
'Yan sanda a Indiya sun ce a kalla mutum 22 sun mutu, wadanda yawancin su yara ne, sakamakon faduwar wata katanga ana tsakiyar shagalin biki a yammacin birnin Jaipur. Mutum 26 kuma sun samu raunuka, wadanda 15 daga cikin su raunin nasu mai tsanani ne. An hanzarta kai marasa lafiyar asibiti da ke kusa da inda lamarin ya faru don a duba lafiyarsu. Wani dan sanda Anil Tank ya shaida wa manema labarai cewa bakin da suka halarci bikin na tsakiyar rakashewa sai kawai ruwan sama ya sauka, daga bisani kuma sai aka yi wata tsawa mai karfin gaske. To daga nan ne sai mutanen suka nemi wajen fakewa, a nan ne wani bangare na katangar wajen da suke ta zube ta kuma fadi kan mutane da dama. Rahotanni sun ce an jera abincin bikin a kusa da katangar ne. Mista Tank ya ce tsawon katangar ya kai mita 27 yayin da fadinta kuma ya kai inci 12 zuwa 13. Gundumar Bharatpur na da nisan kilomita 200 daga Kudancin babban birnin kasar Delhi.
Turawa zuwa Ka Ajiye comment A Qasa....
Katanga ta kashe 'yan biki 22 a India
Created at 2017-05-11 20:02:25
Tags: Katanga ta kashe 'yan biki 22 a India

0 Rate up Star
Share: F T G
Comments: Katanga ta kashe 'yan biki 22 a India
No Photo
Abdulshakur isah
2017-05-12 05:46:25

Munafatan Allah yakiyaye gaba

ANDROID
MUSICS
VIDEOS

Old school Swatch Watches