Kotun kolin kasar Indiya ta fara sauraron
dumbin kararrrakin da suke kalubalantar saki
uku nan take.
Kotun ta ce za ta yi bincike ta gani ko yin saki
uku a lokaci guda na da nasaba da addinin
Musulunci.
Kasar Indiya na daya daga cikin kasashen
duniya kalilan da Musulmi zai iya sakin
matarsa cikin dakika daya muddun ya furta
kalmar 'saki' sau uku.
Sai dai masu fafutuka sun ce yin hakan "nuna
wariya ce."
Kungiyoyin Musulmai da dama na yin suka a
kan tsoma bakin kotun a al'amuran addini,
duk da cewa batun na samun goyon-baya
daga gwamnatin kasar ta Firai Minista
Narendra Modi.
An samu alkalai biyar daga addinai daban-
daban da suka shiga cikin wannan batu mai
sarkakiya, daga addinin Hindu, da Sikh, da na
Kirsta da Zoarastrian da kuma Musulunci.
Alkalan sun tattara takardun kara da dama na
mata Musulmai da kuma kungiyoyin kare
hakki domin gudanar da bincike a kan batun.
A shekarar da ta gabata ne, daya daga cikin
wadanda suka shigar da kara Shayara Bano,
ta yi hira da BBC cewa, inda ta soki lamarin
sakin mai cike da ce-ce-ku-ce.
A watan Oktobar shekarar 2015 ne, wata
mace mai shekara 35 da yaranta biyu, ta tafi
gidan iyayenta da ke Uttarakhand a arewacin
kasar don duba lafiyarta, bayan da ta karbi
takardar saki daga wurin mijinta.
Ta yi kokarin ta samu mijin nata wanda suka
yi shekara 15 tare, wanda yake zaune a birnin
Allahabad, sai dai hakan bai yiwu ba.
Ta shaidawa BBC cewa, "Ya kashe wayarsa,
kuma ba ni da wata hanyar da zan same shi.
Wannan rashin lafiyar na damuna saboda
rayuwar yarana na cikin wani hali."
A watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne,
ta shigar da kara kotun kolin inda take
bukatar a haramta saki uku, wanda hakan zai
ba wa Musulmai maza damar su rika rike
matansu da mutunci".
Duk da an shafe shekaru da dama ana yin
saki uku a lokaci guda, matsayar Malamai da
dama ita ce cewa ba a samu wani
ingantaccen nassi daga Kur'ani ko Shari'a ba.
Malaman addinin Musulunci sun ce, Kur'ani
ya yi bayani karara a kan sha'anin saki, kuma
za a yi zaman wata uku (idda) wanda hakan
zai ba wa ma'aurata damar sasanta
tsakaninsu.
Masu fafutuka sun ce, yawancin kasashen
Musulmai da suka hada da kasar Pakistan da
Bangladesh, sun haramta saki uku a lokaci
guda, amma kuma abin na dada bunkasa a
Indiya.
A shekarun baya-bayan nan, Musulmai maza
da dama na kasar Indiya sun fadawa matansu
cewa za su sakesu ta hanyar aika takarda ko
wayar tarho, ko ma ta sakon wayar salula.
Abin da mafi yawan Malamai suka yi amanna
da shi shi ne cewa, duk da dai Ubangiji ya
halatta saki, to ba ya farin ciki da a yi shi ko
da sau daya ne, in dai ba kan al'amari mai
sauki ba.
Turawa zuwa Ka Ajiye comment A Qasa....
Kotun kolin India za ta sauya dokar saki ukuCreated at 2017-05-11 10:53:06
Tags: Kotun kolin India za ta sauya dokar saki uku 0
Rate up Star Share: